1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar Jamhuriyar Nijar tana daukan sabon salo

October 3, 2013

A Jamhuriyar Niger wani matakin da gwamnatin kasar ta dauka na tsige babban magajin garin birnin yamai Malam Omar Dogari.

https://p.dw.com/p/19tDs
Hoto: DW

A Jamhuriyar Niger wani matakin da gwamnatin kasar ta dauka na tsige babban magajin garin birnin yamai Malam Omar Dogari ya sake aifar da wani sabon cecekuce tsakanin bangaran masu milki da jamiyyar LUMANA Afirka wacce ta fice daga kawancan da ke milki na MRN yau da
yan makonni; Gwamnatin dai na zargin magajin garin da taka dokokin tsarin aikin ofisoshin magadan gari; To amma jam'iyyar lumana Afirka wacce tsohon magajin birnin garin na Yamai ke daya daga cikin kusoshinta na cewa bita da kullin siyasa ne kawai.

Taron majalissar ministocin ranar litanin din da ta gabata ne ya dauki matakin tsige Babban magajin garin birnin na yamai Malam Omar Dogari daga kan mukaminsa; matakin ya biyo bayan wani rahoto ne da ministan cikin gida ya rubuta da ke nuna cewa magajin garin birnin na yamai ya
aikata laifuka da dama na tafiyar da aiki da su ka hada da ciwoma ofishin nasa basuka ba a kan ka'ida ba da dai wasu laifufuka na daban kamar dai yadda ministan shari'a kuma kakakin gwamnatin Malam Moru
Amadu ya yi karin bayani lokacin wani taron manema labarai da ya kira.

Wasu rahotanni dai na cewa ko baya ga tsige magajin garin birnin na Yamai gwamnatin kasar ta Nijar na shirin kama shi domin gurfanar da shi a gaban kotu; To sai dai dangane da wannan batu Minista Kakakin gwamnatin kasar ta Nijar ya ce a halin yanzu dai maganar ba ta kai can ba.

A cikin mayar da martani a kan wannan mataki jam'iyyar Lumana Afirka wacce tsohon magajin garin birnin na Yamai ke daya daga cikin jiga-jagai ta bakin shugaban jam'iyyar reshen birnin Yamai Malam
Sumana Sanda cewa ta yi duk zargin da ake yima Omar Dogarin ba gaskiya bita da kullin siyasa ne kawai.

Niger Uranabbau
Hoto: Getty Images


Yanzu haka dai hukumomin birnin na Yamai sun jibge tarin jami'an a tsaro dauke da kulake a gaban harabar ofishin magajin garin birnin na
Yamai matakin da za a iya fassara shi da neman taka birki ga duk wani yinkurin da tsohon magajin garin na shiga ofis din nasa da jam'iyyarsa tasa ta yi ikrari; Masu sharhi akan alamurran siyasar na ganin Matakin tsige magajin garin birnin na Yamai wata manuniya ce ga irin danbarwar siyasar da ke jiran kasar.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohamadou Awal Balarabe