Siriya: Yarjejeniyar tsagaita wuta na aiki | Labarai | DW | 29.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya: Yarjejeniyar tsagaita wuta na aiki

Amirka da Rasha na ci gaba da bayyana gamsuwa da yadda ake ci gaba da mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta a Siriya yini uku bayan soma aiki da ita.

Amirka da Rasha na ci gaba da bayyana gamsuwa da yadda ake ci gaba da mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta a Siriya ke a yini na uku na soma aiki da ita, wannan kuwa duk da zargin keta haddin yarjejeniyar da bangarorin da ke hamayya da juna a kasar ke yi wa juna.

A jiya Lahadi Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta yi amfani da kyakyawan yanayin da ake ciki a halin yanzu a kasar ta Siriya domin kai kayan agaji ga mutane sama da dubu 150 a garuruwan kasar wadanda mayakan gwamnati ko kuma na 'yan tawaye suka killace.

Rahotanni daga kasar ta Siriya na cewa a manyan biranen kasar jama'a sun samu sukunin fitowa kan tituna a jiya Lahadi da ma yin cefane na kayayyakin masarufi.