Siriya: Sojojin gwamnati sun yi nasara a Homs | Labarai | DW | 06.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya: Sojojin gwamnati sun yi nasara a Homs

Bayan wata fafatawa da aka jima ana yi tsakanin dakarun gwamnatin Siriya da 'yan jihadi a kasar, sojojin gwamnati sun yi nasarar kwato yanki na karshe da ya rage a hannun IS a jihar Homs da ke tsakiyar kasar.

Syrien Waffenruhe Homs (Getty Images/AFP/M. Taha)

Sojojin siriya sun kwace yankin Homs daga hannun mayakan IS

Hakan zai ba sojojin na Bashar Al-Assad damar buda hanya zuwa yankin gabashin kasar domin kakkabe 'yan jihadin da ke wannan bangare a cewar kungiyar nan da ke sa ido kan batun 'yancin dan Adam a kasar ta Siriya. An dai yi mugunyar fafatawa da manyan bindigogi tare da ban-hannu da jiragen yakin kasar Rasha, kafin sojojin Assad su samu kwace birnin Al-Sukhna a cewar kungiyar ta kare hakin dan Adam.

Birnin na Al-Sukhna na a nisan kilomita 70 a arewa maso gabashin birnin nan mai tarihi na Palmira, wanda kuma ke a matsayin birni na karshe bisa hanyar Deir Ezzor a gabashin Siriya, inda 'yan jihadin suka killace mayakan da ke goyon bayan gwamnatin ta Siriya tun daga watan Janairu na 2015.