1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya ta shiga taron Arab League

Abdourahamane Hassane
May 15, 2023

Kasar Syria ta kawo karshen kebewar diflomasiya sama da shekaru goma a cikin kungiyar hadin kan kasashen Larabawa.

https://p.dw.com/p/4RMye
Ägypten «Vollwertiges Mitglied»: Assad-Regierung zurück in Arabischer Liga
Hoto: Ahmed Gomaa/Xinhua/IMAGO

Wakilan kasar Siriyar na halartar wani zaman share fage gabanin taron kolin da za a yi ranar Juma'a a Saudiyya. Wannan dai shi ne karo na farko da jami'an kasar ta Siriya ke halartar taron kungiyar kasashen Larabawa tun watan Nuwamban shekarar ta 2011, lokacin da kungiyar  ta dakatar da gwamnatin Bashar al-Assad, saboda murkushe masu zanga-zangar da ta rikide zuwa rikici da ya barke. Wanda ya yi  sanadin mutuwar mutane sama da dubu 500,000 tare da raba miliyoyi da muhalinsu