Siriya: Kokarin samar da kayan agaji a Aleppo | Siyasa | DW | 11.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Siriya: Kokarin samar da kayan agaji a Aleppo

Majaliyar Dinkin Duniya ta nemi kasar Rasha ta kara wa'adin dakatar da bude wuta domin samun shigar da kayayakin agaji zuwa birnin Aleppo.

Kasar Rasha ta ce a shirye ta ke ta tattauna kan batun kara wa'adin na wasu awoyi uku a birnin Aleppo domin bai wa ma'aikatan agaji damar gudanar da ayyukansu a cewar Majalisar Dinkin Duniya wadda ita kuma ke neman karin wa'adin na kwanaki biyu domin a samu shiga da kayayakin agaji ya zuwa birnin na Aleppo.

A ranar Laraba ce dai rundunar sojojin kasar ta Rasha ta sanar da dakatar da hare-haren da take kai wa ta sama daga karfe bakoye na safe zuwa karfe 10 agogon GMT a wani mataki na tabbatar da cewa motocin agajin da ke shiga birnin na Aleppo sun samu cikeken tsaro. Sai dai a cewar Majalisar Dinkin Duniya wannan mataki da Rasha ta dauka ita kadai, ba zai bada damar samun isheshen lokacin shigar da kayayakin agaji zuwa ga mabukatan ba. Akalla dai mutane miliyn daya da rabi ne ke can a makale tsakanin wuta da wuta a birnin na Aleppo.

Sauti da bidiyo akan labarin