Siriya: Kakkabo jirgin Rasha | Labarai | DW | 01.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya: Kakkabo jirgin Rasha

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta tabbatar da cewa 'yan tawayen Siriya sun kakkabo wani jirginta mai saukar ungulu a gundumar Idlib.

'Yan tawayen Siriya sun kakkabo jirgin Rasha mai saukar ungulu.

'Yan tawayen Siriya sun kakkabo jirgin Rasha mai saukar ungulu.

Rahotannin daga ma'aikatar tsaron ta Rasha sun kuma tabbatar da cewa baki dayan sojojin Rashan da jami'an kasar da ke cikin jirgin su biyar sun rigamu gidan gaskiya. Shi dai wannan jirgi mai saukar ungulu na Rashan kirara Mi-8, ana amfanin da shi ne wajen raba kayan agaji a Aleppo da aka killace, wanda kuma fararaen hula da ke cikin birnin ke cikin matsanancin hali. 'Yan tawayen Siriyan da ke yankin Kudu maso Yammacin birnin na Aleppo na ci gaba da kai hare-hare a kan dakarun gwamnati, wadanda a 'yan kwanakin nan da taimakon Rashan suke neman cin karfinsu tare da kwace iko da birnin na Aleppo baki daya.