Siriya: Hari ya ritsa da masu kai agaji | Labarai | DW | 20.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya: Hari ya ritsa da masu kai agaji

Dakarun gwamnatin Siriya sun kai hari ta sama a kan motoci da ke shigar da kayan agaji, bayan sanar da cikar wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta.

Bisa ga dukkanin alamu dai, yarjejniyar tsagaita wuta a Siriya na ci gaba da tabarbarewa, inda rahotannin da ke fitowa da ga birnin Aleppo ke cewar dakarun gwamnati sun bude wuta a kan ayarin jami'an kai kayan agaji, kana kungoyoyi sun ce harin bama-bamai ta sama ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 32.

Wata kungiya da ke sa ido da kare hakkin bil'adama a Siriyar, ta ce kawo yanzu babu adadin wadanda suka jikkata da kuma dimbin asarar da aka samu a harin.Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da harin da ke haddasa fargabar rushewar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin dakarun gwamnatin da 'yan tawaye.