Siriya: An hallaka mutane 43 | Labarai | DW | 22.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya: An hallaka mutane 43

Kimanin mutane 43 ne aka bada labarin rasuwarsu biyo bayan wasu hare-hare da aka kai da jiragen sama a wasu yankuna da ke kudancin Kasar Siriya.

Bayanai na kara fitowa fili game da harin nan da aka kai wasu yankunan kasar ciki har da Idlib da ke kasar Siriya inda 'yan tawaye suka zargi gwamnatin Bashar al-Assad da dakarun Rasha da yin amfani da jiragen yaki wajen afkawa mutane.

Zuwa yanzu dai mutane 43 wanda galibisu fararen hula ne aka ba da labarin rasuwarsu, baya ga wasu da dama da suka jikkata a wata kasuwa da jama'a da dama kan ziyarta a yankin nan na Maaret al-Numann.

Kungiyar nan da ke sanya idanu kan kare hakkin dan Adam a kasar ta ce baya ga wanda suka jikkata da wanda suka rasu, akwai wasu da dama da baraguzan gine-gine suka rufe wanda ba a san halin da suke ciki.

To sai dai dakarun Rasha sun musanta hannu a wannan harin wanda 'yan adawa da ke yaki da gwamnati suka ce shi ne mafi muni da aka samu a yankin a dan tsakanin nan.