Siriya: Amirka na sintirin hadaka da Turkiyya | Labarai | DW | 08.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya: Amirka na sintirin hadaka da Turkiyya

Kasashen Amirka da Turkiyya, sun kaddamar da wani sintiri na hadin gwiwa a yankin arewa maso gabashin kasar Siriya.

Hakan dai wani kokari ne na sassauta rikicin da ke tsakanin kasashen kan mayakan Kurdawa a Siriya.

A karon farko an ga wasu motocin sulke daga Turkiyya da suka ratsa iyaka don hadewa da na Amirka wajen aiki tare bayan nasarar cimma wata yarjejeniya.

Shaidu sun ce an ga wasu jiragen Helikofta biyu da suka yi rakiyar motocin na yaki, lokacin da suke ratsa katangar da ke kan iyakar Turkiyyar da kuma Siriya.

Yarjejeniyar da aka cimma a ranar bakwai ga watan Augusta, na da burin samar da tudun mun tsira a iyakar Siriya da kuma Turkiyyar gabas da wani kogin da mayakan Kurdawa ke iko da shi.