1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta zargi shugaba Emmanuel Macron na Faransa

Zulaiha Abubakar
October 10, 2019

Dubban al'ummar Siriya na ficewa daga gidajensu sakamakon harin da Turkiyya ta kai wa mayakan Kurdawa a Arewa maso Gabashin kasar, bayan kasar Amirka ta sanar da janye sojojinta daga yankin na Kurdawan Siriya.

https://p.dw.com/p/3R5nL
Türkei PK Außenminister Mevlut Cavusoglu
Hoto: AFP/A. Altan

A wani cigaban kuma ministan harkokin kasashen ketare na Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya zargi shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da raba kasar Siriya, bayan Faransan ta yi Allah wadai da harin da dakarun Turkiyyan suka kai wa Kurdawan.

Kasashe da dama sun tsoratar game da yiwuwar tserewar 'yan kungiyar IS da ke tsare a gidajen yarin Siriya sakamakon wannan hari, duk kuwa da cewar shugaban kasar Bashar al-Assad ya dauki alwashin daidaita al'amura cikin kankanin lokaci.