Shugabannin Turayyar Turai sun amince da zabtare kasafin kudi | Labarai | DW | 08.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin Turayyar Turai sun amince da zabtare kasafin kudi

Shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun amince da zabtare kasafin kudin kungiyar da kashi uku cikin 100

A wannan Jumma'a, Shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun amince da zabtare kasafin kudin kungiyar da kashi uku cikin 100, abun da ke zama karo na farko da su ka amince da irin wannan mataki cikin shekaru 60 da su ka gabata.

Yayin taron kungiyar wanda ke gudana a birnin Brussels na kasar Belgium, shuganannin tabbatar da cimma wannan matsaya, bayan tattaunawa ta tsawon lokaci tsakanin Firaministan Birtaniya David Cameron da goyon Shugaban gwamnatin Jamus Angela Merkel.

Matakin zabtare zai fara aiki daga kasafin kudin kungiyar na gaba na shekara ta 2014 zuwa 2020. Tuni shugabannin kasashe na kungiyar su ka nuna gamsuwa da cimma wannan matsaya. Firaministan Birtaniya David Cameron da shugaban Faransa Francois Hollande su ka fara yin maraba da matakin. Shugaban hukumar gudanar kungiyar ta Tarayyar Turai Herman Van Rompuy ya nami majalisar dokokin kungiyar ta yi abun da ya dace wajen amince da kasafin kudin, bayan cimma matsayin shugabannin kasashen kungiyar 27.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu