Shugabannin Taliban na ziyara a Rasha | Labarai | DW | 09.07.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin Taliban na ziyara a Rasha

Kungiyar mayakan Taliban a kasar Afghanistan sun karbe kaso mafi tsoka na lardunan kasar.

Sa'oi kalilan bayan shugaba Joe Biden na Amirka ya sanar ranar kammala janye dakarun kasarsa daga Afghanistan, kungiyar Taliban ta yi ikirarin mallakar iko da kaso tamanin da biyar cikin dari na lardunan kasar.

A wata ziyara da jagororin kungiyar Taliban din suka kai a birnin Mascow, mai magana da yawunta  Zabihullah Mujahid ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa sun karbe ikon yankuna kusan 250 cikin 398 na yankunan kasar.

A lokacin da yake sanar da kammala ficewar a ranar 31 ga watan Ogusta, shugaba Biden ya ce lokaci ya yi da za a baiwa al'ummar kasar ta Afghanistan dama domin su nemawa kansu makoma.