Shugabannin Afirka za su tattauna batun Boko Haram | Labarai | DW | 08.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin Afirka za su tattauna batun Boko Haram

Shugabanin ƙasashen yankin yammaci da na tsakiya na Afirka za su tattauna a birnin Malabo na Equatorial Guinea.

Taron wanda aka shirya zai samu halartar shugabannin daga ƙasashen Nijar da Kamaru a Chadi da Najeriya, na da manufar ƙaddamar da wani tsarin na bai ɗaya na haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen.

Domin yaƙi da Ƙungiyar Boko Haram wacce ke kai hare-hare na ta'addanci a cikin ƙasashen Najeriyar da Nijar da Kamaru da kuma Chadi. A wani rahoton da ta bayyana Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce tashin hankali na Boko Haram a cikin shekaru shida ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 15 a Najeriyar.