Shugaban Yemen da ke gudun hijira ya koma gida | Labarai | DW | 17.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Yemen da ke gudun hijira ya koma gida

Shugaba Abd Rabbo Mansour Hadi na Yemen wanda ya kwashe watanni shida yana gudun hijira a Saudiyya bayan da 'yan tawayen Houthis suka kore shi ya koma gida a wannan Talata

A Yemen Shugaban kasar Abd Rabbo Mansour Hadi wanda ke zaman gudun hijira watanni shida a kasar Saudiyya ya koma gida a wannan Talata.

Fadar shugaban kasar wacce ta tabbatar da wannan labari ta ce sabkarsa a birnin na Aden daga jirgi ke da wuya Shugaba Mansour Hadi ya yi tsinke zuwa fadarsa inda ya koma kan aikinsa tare da soma bayar da umarni kan harin da dakaransa suka soma kaddamarwa a jiya Litanin a wani mataki na neman kwato birnin Taez daga hannun 'yan tawayen kasar wadanda ke rike da jihohin yankin Arewacin kasar da suka hada da babban birnin kasar Sana'a.

Shugaban kasar ta Yemen Abd Rabbo Mansour Hadi ya koma a birnin na Aden kwanaki biyu bayan dawowar Firaministansa Khaled Bahah.