1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Ukraine zai gana da Putin

Yusuf BalaOctober 12, 2014

Shugaba Poreshenko ya ce zai gana da shugaban na Rasha ganin yadda ake samun raguwar kai hare-hare daga bangare 'yan aware da ke samun goyon bayan kasar.

https://p.dw.com/p/1DTr1
Belgien Petro Poroschenko in Brüssel 30.08.2014
Hoto: Reuters

Rikicin gabashin Ukraine da yarjejeniyar tsagaita wutar da ke cike da rudani sune za su zama manyan batutuwa da za'a tafka muhawara a kansu cikin babban taron da zai gudana wannan mako mai kamawa, a wani zama da ba kasafai ake yi ba tsakanin shugaba Petro Poroshenko da shugaba Vladimir Putin na Rasha.

Wannan dai na zama wani yunkuri da ke bude sabon babi na sake nazarin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka yi a baya, wacce ke cike da karya sharuda a karo daban-daban.

'Yan tawayen masu samun goyon bayan kasar ta Rasha da dakarun kasar ta Ukraine a yankin Doneskt da ke gabashin kasar, sun amince da daukar wani lokaci ba tare da kai wa juna hari ba sannan dakarun sojin sun bayyana cewa an samu ci gaba a yarjejeniyar.

Mahukuntan na Kiev dai na zargin kasar ta Rasha da iza wutar rikici a yankunan na Doneskt da Lugansk a kasar ta Ukraine ciki kuwa har da tura dakarun ta a wasu yankuna da gwamnati ba ta da iko a kansu .

Shugaba Putin da Poreshenko za su gana ne a ranar Juma'a a karon farko, tun ganawar watan Agusta a lokacin da za su halarci babban taron kasashen Asiya dana turai (ASEM) a Milan.