Shugaban Najeriya ya nuna taka tsantsan kan sasantawa da Boko Haram | Labarai | DW | 16.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Najeriya ya nuna taka tsantsan kan sasantawa da Boko Haram

Shugaban Najeriya ya jaddada shirin gwamnatinsa na tattauna kan sako 'yan matan da ake garkuwa da su.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya wanda yake kammala ziyarar aiki a kasar Faransa ya kara jaddada shirin gwamnatin kasar na tattauna da Boko Haram kan yadda za a sake 'yan mata 'yan makaranta na Chibok da tsagerun kungiyar suke garkuwa da su fiye da shekara guda da ta gabata. Kalaman shugaban na zuwa yayin da dakarun kasar ke samun nasara a yaki da tsagerun na kungiyar ta Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

A cikin hira da tashar talabijin ta Faransa Shugaba Buhari ya ce duk wata tattauna tilas a tantance wadanda za su wakilci kungiyar:

"Haka yana kara zama mai wahala, dole mu tantance wadanda suke ikirarin shugabancin Boko Haram, shin shugabannin ne na gaskiya kuma yaya tasirinsu a cikin kungiyar. Kuma sun san inda 'yan mata suke da halin da suke ciki. Amma kawai kowani dan kungiyar Boko Haram ya nemi gwamnati domin cewa shi shugaba ne da zai iya sako 'yan matan, dole mu yi taka tsantsan a kai."

A wannan Laraba Shugaban na Najeriya ya kammala ziyarar aikin a kasar ta Faransa.