1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Koriya ta Arewa ya kai ziyara China

Suleiman Babayo MNA
June 19, 2018

Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa yana ziyarar aiki karo na uku a kasar China inda ya gana da Shugaba Xi Jinping.

https://p.dw.com/p/2zomb
Singapur Kim Jong-Un und Donald Trump Fahrzeuge
Hoto: picture-alliance/dpa/Kyodo

Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya fara ziyarar aiki karo na uku a kasar China, inda ake sa ran zai shaida wa Shugaba Xi Jinping na China abubuwan da suka cimma lokacin ganawa da Shugaba Donald Trump na Amirka a makon da ya gabata.

Karo na uku ke nan da shuganan na Koriya ta Arewa yake kai ziyara China. Ita dai China ta kasance kasa mafi tasiri kan diplomasiyya da tattalin artziki ga Koriya ta Arewa.

Wannan ziyara tana zuwa lokacin da kasashen Amrika da Koriya ta Kudu suka amince da jingine shirin atisaye na soja tsakanin kasashen biyu, abin da ke zama daya daga cikin bukatun Koriya ta Arewa da aka tattauna lokacin da aka yi ganawa mai tarihi a Singapore tsakanin Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa da Shugaba Donald Trump na Amirka.

Kafofin yada labarai na China sun ce shugaban na Koriya ta Arewa zai kwashe kwanaki biyu yana ziyarar.