Shugaban hukumar WFP ya isa Janhuriyar NIger | Labarai | DW | 29.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban hukumar WFP ya isa Janhuriyar NIger

A yau ne shugaban hukumar bayar da tallafin abinci na Mdd, wato James Moris ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Janhuriyar Niger.

Wannan ziyara dai ta Morris tazo ne kwanaki kadan bayan gwamnatin ta Niger ta karyata bayanin hukumar da Mr Moris din kewa jagoranci na cewa da alama Janhuriyar ta Niger ka iya fuskantar karancin abinci a shekara ta 2006.

Mr Moris yaci gaba da cewa yaje kasar ta Niger ne don ganin an samu fuskantar juna a game da wannan bayani na hukumar tasa tare da karin bayanin cewa abin da hukumar sa tasa a gaba shine ceto rayuka da kuma bayar da tallafi amma ba wai tara kudade ba.

Mr Moris wanda ya fadi hakan a wata cibiyar kiwon lafiya dake Faga,wacce keda nisan kilomita 15 daga birnin Niamey, ya tabbatar da cewa hukumar sa zata ci gaba da kokarin da take a kasar na ceto mutanen da wannan bala´i na yunwa ya fadawa.

Jim kadan dai bayan tattaunawa da Mer Moris yayi da Faraminista Hamma Amadou, bayanai sun shaidar da cewa kasar ta Niger da hukumar bayar da tallafin ta Mdd zasu ci gaba da aiki kafada da kafada da juna wajen yakar yunwa da kuma Fatara a kasar.

Game kuwa da wannan hali da ake ciki, kafafen yada labaru na kasar sun rawaito ministan ma´aikatar ilimi na kasar wato Ari Ibrahim na fadin cewa bartun Yunwa a kasar ta Niger a yanzu haka ya kasance tsohon labari domin kuwa damina tayi kyau abinci ya wadata.