1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Shugaban Amurka ya caccaki firaministan Isra'ila

Suleiman Babayo ATB
June 3, 2026

Shugaban Amurka ya tabbatar da cewa ya caccaki firaministan Isra'ila ta wayar tarho, lokacin da suka tattauna kan yadda Isra'ila ke hana ruwa gudu wajen kawo karshen rikicin Gabas ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/5EocI
Philippinen Manila 2026 | Protest gegen den Iran-Krieg vor der US-Botschaft
Hoto: Aaron Favila/AP Photo/picture alliance

A cikin wata hira Shugaba Donald Trump na Amurka ya tabbatar da rahotannin ya caccaci Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ta wayar tarho kan yadda yake ci gaba da fada da kungiyar Hezbollah ta Lebanon, abin da yake dagula shirin zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, ganin Iran ta fice daga tattaunawa da Amurka, sakamakon yakin tsakanin Isra'ila da Hezbollah.

Halin da ake ciki na rikici

USA Washington D.C. 2026 | Donald Trump empfängt Benjamin Netanjahu im Weißen Haus
Hoto: Avi Ohayon/GPO/Xinhua/picture alliance

Wannan na zuwa lokacin da dakarun kare juyin-juya hali na Iran sun dauki alhakin harin da aka kai a kasar Kuwait, a matsayin martanin harin da Amurka ta kai kan jirgin ruwan dakon man fetur na Iran.

Hare-haren na Iran da jiragen sama marasa matukasun lalata wani bangaren na babban filin jiragen saman Kuwait, inda mutum guda ya halaka kana wasu fiye da 60 suka jikata. Ita dai Iran tana karfafa martani kan kaddarorin Amurka da ke yankin Gabas ta TSakiya, abin da ke ritsawa da kasashen da suka bai wa Amurka masauki.