1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Amurka za ta karfafa saka hannun jari a Birtaniya

Abdourahamane Hassane
September 17, 2025

Karo na biyu kenan da shugaban Amurka Donald Trump ke kai ziyara a Birtaniya bayan wadda ya kai tare da rakiyar matarsa ​​Melania, inda marigayiya Sarauniya Elizabeth ta biyu ta tarbe shi a watan Yunin 2019.

https://p.dw.com/p/50ac1
Donald Trump da matarsa Melania Trump lokacin da suka isa a filin jirgin sama na Stansted da ke London Hoto: Evan Vucci/AP Photo/picture alliance

Shugaban Amurka Donald Trump ya fara wata ziyarar aiki ta musamman a Birtaniya, tun a yammacin Talata inda zai shafe kwanaki biyu yana ganawa da shugabannin siyasa da na sarauta.

Ana sa ran a kan wannan ziyara, Amurka da Birtaniya za su karfafa hulda da kuma kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.

Tuni dai kamfanin harhada magunguna na Birtaniya GSK ya sanar da cewa zai zuba jari na dala biliyan 30 a cikin shekaru biyar a Amurka.