Shugaba Trump ya caccaki FBI | Labarai | DW | 18.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Trump ya caccaki FBI

Shugaban kasar Amirka Donald trump ya ce hukumar FBI ba ta aikinta, maimakon hakan hukumar na bata lokaci ne wajen tabbatar da zarge-zargen sa hannun Rasha a zaben Amirkar na bara.

Shugaba Donald Trump na Amirka ya caccaki hukumar bincike ta FBI kan harin da aka kai kan dalibai a birnin Florida na kasar. Zafafan kalaman na Mr. Trump dai na zuwa ne yayin da dubban dalibai da iyayensu ke bukatar gwamnatin Amirka a sauya dokar da ta bai wa jama'a ikon mallakar bindiga, bayan kisan dalibai 17 da maharin ya yi. Shugaban na Amirka ya ce hukumar ba ta aikinta, maimakon hakan hukumar na bata lokaci ne wajen tabbatar da zarge-zargen hannun Rasha a zaben Amirkar.

A sakon da wallafa a shafinsa na Twitter ya ce FBI ta koma kan aikinta na kare rayuwar jama'a daga hadari, don ba za a lamunce wa kashe-kashen ba. Bayanai dai sun yi nunin cewa an tsegunta wa hukumar FBI cewar mutumin da ake zargi ya rika ya nuna sha'awarsa da aikata kashe-kashen tun cikin watan jiya, sai dababu wani matakin da ta dauka.