Shugaba Tinubu ya zama dan takarar APC a 2027
May 24, 2026
Zaben fidda gwani na APC ya kasance na ransa sarki ya dade ga Shugaba Tinub, da aka zaba a shekarar 2023, saboda bai taba boye niyyarsa ta tsayawa takara don sake neman wa'adin mulki karo na biyu ba. Tuni dai, kwamitin jam'iyyar APC da ke kula da gudanar da zaben fidda gwani ya tabbatar da nasarar Tinubu, a wani kwarya-kwaryar bikin mika tuta ga dan takara da aka gudanar a gaban 'yan APC da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a Abuja, babban birnin kasar.
Karin bayani: Zaben fidda wani na APC na cike da rikici
Shugaba Tinubu ya yi alkawarin yin aiki don "karfafa sauye-sauyen da aka gudanar, da kuma yin koƙari ba tare da gajiyawa ba don ciyar da Najeriya gaba." Dama dan takara daya tilo ne ya kalubalance shi mai suna Stanley Osifo, wani dan kasuwa da ya fito daga jihar Edo a yankin Kudu maso yammacin kasa, wanda ya samu kuri'u kusan 16,500 daga cikin kuri'u sama da miliyan 11 da aka kada.
Karin bayani: Hadin kan adawa don neman kawar da APC ya ci karo da cikas
Tun bayan da ya hau kan karagar mulki, Bola Tinubu ya aiwatar da jerin sauye-sauyen tattalin arziki da suka kwantar da hankalin masu zuba jari na kasa da kasa, amma ya yi mummunan tasiri ga karfin arzikin 'yan Najeriya, inda hauhawar farashin kayayyaki ya zarta kashi 30% a shekarar 2024.