1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaFaransa

Shugaba Macron na Faransa zai yi tozali da Zelensky

Abdoulaye Mamane Amadou
June 4, 2024

Shugaban Faransa Emmaneul Macron zai karbi bakwancin takarwansa na Ukraine Volodymyr Zelensky a fadar Elysée a kokarin kasar na warware yakin da Ukraine ke fafatawa da Rasha.

https://p.dw.com/p/4ge3Y
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron Hoto: Dimitar Dilkoff/AFP

Shugaba Zelensky zai halarci bukukuwan zagayowar cika shekaru 80 da sojojin kawance suka samu damar shiga Turai a yankin duniya na biyu ta gabar Normandie, kazalika ganawar wata dama ce ga shugabannin biyu da su tattauna muhimman batutuwan da suka shafi yakin kasar Ukraine ke gwabzawa da Rasha.

Ko a wannan Talatar sai da Shugaba Zelensky  ya bayyana a cikin wani sakonsa na rana rana da yake wa 'yan kasar da cewa kan   Rasha na kara matsa kaimin luguden wutar da take yi kan yankin Donetsk ne maimakon Kharkiv