Shugaba Goodluck Jonathan na ran gadi a Kenya | Labarai | DW | 06.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Goodluck Jonathan na ran gadi a Kenya

Duk da irin rikicin cikin gida da dambarwar siyasar da jamiyya mai mulki na PDP ke ciki a Najeriya, shugaban ƙasar ya kai ziyara Kenya dan tattauna hanyoyyin inganta tattalin arziƙi

Titel: DW_Nigeria_Integration2 Schlagworte: Nigeria, Präsident, Goodluck Jonathan Fotograf: Katrin Gänsler Aufnahmedatum: 04. April 2011 Aufnahmeort: Abuja, Nigeria Bildbeschreibung: Präsident Goodluck Jonathan

Shugaba Gooodluck Jonathan

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya na ran gadi a ƙasar Kenya, inda ya gana da sabon shugaban ƙasar Uhuru Kenyatta wanda shi ma a baya ya kai ziyara ga takwaran na sa na Najeriya. A wannan karon dai shugabanin biyu na tattauna yadda zasu inganta dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu musamman a fanin tattalin arziƙi kamar yadda Uhuru Kenyatta shugaban kasar Kenyan ya bayyana

"ƙasashen Kenya da Najeriya sun daɗe suna aiki tare musamman a fagen siyasar ƙasa da ƙasa, kuma mun amincewa cewa yanzu muna so mu ga haɗin kan ya ƙaru a fanin cinikayya tsakanin ƙasashen biyu muna la'akari da cewa kasuwanci tsakanin ƙasashen Afirka a yanzu haka na ƙasa da kashi 12 cikin 100"

Duk da cewa Shugaba Goodluck Jonathan ya bar gida ne a daidai lokacin da jamiyyarsa ta PDP ke fama da rikicin gida shugaban ya jaddada mahimmancin inganta hadin kan da ke tsakanin ƙasashen Afirka

"Akwai buƙatar ƙasashen Afirka su yi aiki da juna, kuma ya ma fi mahimmanci tsakanin Kenya da Najeriya saboda Najeriya ta kasance a yammacin Afirka inda take kusa da tekun Atlantic a yayin da ita kuma Kenya wadda take gabashin Afirka tana kusa da tekun Indiya kuma mun yi imanin cewa idan har akwai taimakekeniya a tsakaninsu, ba ƙasashen mu biyu kaɗai zamu taimakawa ba, zamu taimakawa nahiyar Afirka baki ɗaya"

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe