Shugaba Buhari zai rika aiki daga gida | Labarai | DW | 26.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Buhari zai rika aiki daga gida

Shugaban zai ci gaba da aiki daga gida ne kasancewar ya nemi duk takardun da ke bukatar dubawarsa a kai masa su gida a cewar minista, yayin da ya gaza zama da ministocinsa.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya gaza halartar taron majalisar ministocin kasar a karo na biyu kamar yadda wani baban minista a kasar ya bayyana a wannan rana ta Laraba, lamarin da zai sake bude sabon babi a dangane da lafiyar Shugaban.

Shugaba Buhari dai da ya kwashe kusan watanni biyu a birnin London inda ya je jinya tun a farkon wannan shekara, ya gaza zuwa taron ne domin ya nuna bukatar ya na so ya huta kamar yadda ministan yada labarai Lai Mohammed ya bayyana.

Mataimakin shugaban na Najeriya Yemi Osinbajo da ya kasance mukaddashin shugaban na Najeriya a lokacin da Shugaba Buhari  dan shekaru 74 ya je jinya, shi ya wakilici shugaban a zaman da aka yi da ministocin kamar yadda ministan yada labaran Lai Mohammed ya bayyana wa manema labarai.

Shugaban zai ci gaba da aiki daga gida kasancewar ya nemi duk takardun da ke bukatar dubawarsa a kai masa su gida a cewar ministan. Taron majalisar ministocin da aka yi dai na karshe na zama ranar 16 ga watan nan na Afrilu kuma Shugaba Buhari bai halarta ba ko da ya ke ministan yada labaran ya ce wasu dalilai ne na daban suka sa bai halarta ba.