Shugaba Buhari zai koma gida | Labarai | DW | 12.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Buhari zai koma gida

Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce ya shirya don komawa gida Najeriya, bayan tabbatar da samun lafiya da ya yi a zaman jinyarsa a Birtaniya.

Wata sanarwa daga fadar shugaban kasa a wannan Asabar, ta ce abin kawai da ya saura masa shi ne amincewar likitocin shugaban wadanda sai da izininsu ne Buharin ya ce zai kama hanya. 'Yan Najeriyar da dama dai na kokonton ko shugaban mai shekaru 74 na da karfi da lafiyar jagorantar kasar. Ko a 'yan kwanakin na ma dai an gudanar da zanga-zangar neman ko ya koma aiki, ko kuma ya yi murabus saboda halin lafiyar ta sa. A bana dai kwanakin da shugaba Buhari ya yi a Birtaniya sun zarta wadanda ya yi a Najeriyar.