1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Buhari ya bukaci sojoji su jajirce

Abdullahi Tanko Bala
November 28, 2018

A matakin karfafa gwiwa ga sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci sojojin a Maiduguri inda ya bukaci su jajirce wajen yaki da'yan Boko Haram.

https://p.dw.com/p/395dO
Nigeria Präsident Muhammadu Buhari bei Militär in Maiduguri
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci sojojin kasar su jajirce wajen yaki da Boko Haram duk da rashin takwarorinsu da suka yi a harin da 'yan Boko haram suka kai musu a baya bayannan.


Shugaban ya kai ziyara Maiduguri a arewa maso gabashin kasar inda ya gana da sojojin tare da jajanta musu da kuma karfafa musu gwiwa yana mai yaba kwazo da sadaukarwar sojojin wajen kare al'ummar kasa da cigabanta.


Ziyarar na zuwa ne kwana daya gabanin shugaban na Najeriya ya nufi Ndjamena domin tattaunawa da takwaransa na Chadi shugaba Idris Deby game da yaki da 'yan kungiyar Boko Haram.