1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya: Cimma yarjejeniya a Tunusiya

Mahmud Yaya Azare LMJ
November 13, 2020

Bangarorin da ba sa ga maciji da juna a kasar Libiya, sun amince da shirin da aka gabatar yayin tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta na ficewar sojojin haya daga kasar.

https://p.dw.com/p/3lGHC
Bildkombo Haftar und as-Sarradsch
Janar Khalifa Haftar da shugaban gwamnatin hadin kan kasar Libiya Fayez al-Sarraj

Bayan sun kwashe kwanaki biyar suna zazzafar muhawara da juna a taron sulhu da suke gudanarwa a kasar Tunusiya, wakilan bangarorin da ke yakar juna a Libiya sun cimma yarjeniyoyin da ake sa ran za su kawo karshen rikicin kasar na tsawon shekaru, duk da tarin kalubalen da ke tattare da aiwatar da wadannan yarjeniyoyin.

Karin Bayani: Taron magance rikicin Libiya

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta wucin gadi kan kasar Libiyan Stephanie Williams ce ta shaidawa manema labarai hakan: "An cimma amincewa da gudanar da tsabtataccen zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa cikin tsukin watanni 18 da ke tafe. An kuma amince da kafa rundunar sojojin hadin gwiwa da za ta maye gurbin wadda ake da ita a yanzu ta bangarori mabanbanta, gami da amincewar kowane bangare da janye sojojin haya da mayakan sa kai a dukkanin yankunan, lamarin da zai share fagen cimma dakatar da bude wuta mai dore wa a fadin Libiya."

Schweiz Genf | Gespräche zu Waffenstillstand in Libyen - Stephanie Williams
Stephanie Williams wakiliyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya a LibiyaHoto: Fabrice Coffrini/AFP/Getty Images

To sai dai tun ba a je ko ina ba, shugabar kwamatin shirya kundin tsarin mulkin kasar, Stephanie Williams ta ce yarjejeniyar ta Tunusiya na shirin maimaita irin kuskuren da aka tafka a yarjejeniyar Sukairat ta kasar Maroko, wacce aka cimma shekaru biyar da suka gabata, amma ta gaza cirewa 'yan kasar ta Libiya kitse daga wuta.

Karin Bayani: Tsagaita wuta a Libiya

Suma a nasu bangaren, magoya bayan Janar Khalifa Haftar da ya jima yana hankoron ganin ya mallaki kasar da karfin tuwo, sun nuna cewa duk wata yarjejeniyar da za ta kai ga damka mulkin Libiya a hanun 'yan ta'adda, to ya kamata a kwan da sanin cewa al'ummar Libiya za su bijire mata. Dhau Mansur guda ne daga cikin na hanun daman Janar Haftar din: "Wani sabon tsari dake kokarin tsinka igiyar fahimtar junan da ake neman cimma yarjejeniya kanta shi ne, yin rufa-rufa da ake wajen fayyace irin jagogorin da ya halatta su mulki Libiya. Idan aka bar wannan gabar haka kara zube, to kasashen ketare ne za su nada mana shugabanni ba al'ummar Libiya ba."

Cimma yarjejeniyar kafa sansanin dakarun sojojin kasar Qatar a birnin Misrata da gwamnatin hadin kan kasar ta Libiya da ke birnin Tripoli ta yi, a daidai lokacin da wakilan bangarorin ke tattaunawa wannan yarjejeniyar a Tunusiya, ya sanya Masaharhanta na ganin cewa, lalle har yanzu da sauran rina a kaba kan warware rikicin na Libiya.