1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan kawo karshen yakin Libiya

Mahamud Yaya Azare
June 8, 2020

Ana ci gaba da mai da martini dangane da shirin da shugaban Masar Abdulfattah al-Sisi ya gabatar, da zai taimaka a kawo karshen yakin basasar kasar Libiya.

https://p.dw.com/p/3dS1H
Libyscher Militärbefehlshaber Khalifa Haftar mit dem ägyptischen Präsidenten Abdel Fattah al-Sisi im Präsidentenpalast in Kairo
Jagoran 'yan tawayen Libiya Khalifa Haftar da Shugaba Abdel Fattah al-Sisi na MasarHoto: Reuters

A wannan Litinin din ake sa ran shirin zai fara aiki da tsagaita wuta a fadin kasar ta Libiya, domin share fagen tattaunawar zaman lafiya. Shirin da shugaban na Masar Abdulfattah al-Sisi ya kaddamar da shi tare da goyon bayan madugun 'yan tawayen na Libiya janar Khalifa Haftar dai, shugaban majalisar dokokin kasar da wa'adinta ya kare Akilah saleh na saka ran zai samu karbuwa ga illahirin 'yan kasar da yakin shekaru ya kassara.

Nasarar dakarun gwamnati

Janar Haftar wanda dakarunsa ke shan kashinsu a hanun dakarun gwamnatin Libiyan da kasar Turkiyya ke dafa musu, ya ce wannan shirin ba zai yi aiki ba muddin Turkiyya ba ta fice a kasar ba.

Libyen zerstörtes Gebäude in Tripoli
Asarar rayuka da dukiyoyi a LibiyaHoto: Imago

A nata bangaren, gwamnatin hadin kan kasar ta Libiya da dakarunta ke ci gaba da baza ikonsu a yammaci da kudancin kasar, ta ce babu batun tsagaita wuta akan wannan gabar da dakarunta ke murkushe 'yan tawaye. Koda yake gwamnatin ta ce a shirye take da duk wani tsarin tattaunawar zaman lafiya, amma ba tare da Janar Haftar da ya kai hare-hare a fadar mulkinta da suka halaka daruruwan 'yan kasar kana yake neman wargaza Libiyan ba.

Maraba da matakin al-Sisi

Tuni dai wasu daga cikin gwamnatocin kasashen Larabawan yankin Tekun Fasha musamman wadanda ake zargi da taimakawa madugun 'yan tawayen na Libiya Janar Haftar da suka hadar da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain da kuma Jordan suka yi na'am da shirin na al-Sisi. A yayin da Amirka wacce take baya-baya da rikicin na Libiya da kuma Rasha, suka bayyana shirin na al-sisi da cewa abun a saurara ne da kunnan basira, suma kasashen da ke makwabtaka da Libiyan musammama Tunusiya da Aljeriya cewa suka yi suna maraba da duk wani shirin da zai dawo da zaman lafiya a makwabciyar tasu. Ita kuwa Maroko na cewa, yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a birnin Sukhairat na kasarta da ta kai ga kafa gwamnatin hadaka, ita ce tushen duk wani shirin zaman lafiyar da za a girka a kasar ta Libiya.