Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin za a ji cewar ana ci gaba da mayar da martani kan kiran da gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya yi na hana zirga-zirgar makiyaya daga arewa zuwa kudancin Najeriya.
Adadin wadanda suka rasa rayukansu, sakamakon rikicin da ya kunno kai tsakanin manoma da makiyaya a jihar Plateau da ke yankin Arewa maso Tsakiyar Najeriya na karuwa.
Al'ummar jihar Kano da wasu jihohin arewacin Najeriya da ake fama da masu amfani da makamai suna kwacewa mutane wayoyin hannu na salula, sun fara yunkurin daukar doka a hannunsu kan wadanda aka zarga da satar wayar.
Engr. Abba Kabir Yusuf na Jam'iyyar NNPP ya lashe zaben gwamnan jihar Kano inda ya ka da abokin hamaiyarsa na APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna. Tuni dan takarar APC din ya yi wa sabon zababben gwamnan fatan alheri.
Rundunar 'yansanda a jihar Kano, ta bayar da belin shahararriyar tauraruwar nan ta TikTok mai suna Murja Ibrahim Kunya. An dai kama Murja ne a jajiberin ranar da ta shirya bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta.