Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Ranar yaki da cutar tarin-fuka ta duniya, sannan ana ci gaba da zanga-zanga a Faransa sakamakon kara yawan shekaru da mutum zai yi a bakin aiki kafin yin ritaya.
Tun lokacin da gwamnatin Najeriya karkashi sabon Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta tabbatar da tsarin cire tallafin man fetur ana shiga mawuyacin hali saboda tashin farashin mai da kayayyakin bukatun rayuwa.
Wasu 'yan ta'adda da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun sace makiyaya akalla 30 a wasu kauyuka da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya.
Bisa taimakon Kungiyar Tarayyar Turai, Kwararru a harkar tsaro na kasashe 10 na Sahel da Sahara na duba rawar da fararen hula za su iya takawa a yaki da ta'addanci baya ga matakan soja da ake dauka don tinkarar matsalar.
Harkokin yau da kullum na Nijar da ke makwabtaka da Najeriya na tafiyar hawainiya sakamakon zaben da ya gudana. A Maradi harkokin kasuwanci da zirga-zirgar jama'a sun sukurkuce saboda rufe kan iyakar kasashen biyu.