Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Shirin ya kunshi kokawar da kungiyar Human Rights Watch t yi game da rashin hukunta jami'an tsaron Najeriya da suka ci zarafin matasan da suka yi zanga-zangar EndSARS. A Nijar matsalar tsaro a yankin iyakoki da Mali da Burkina Faso na kara kamari.
Bisa taimakon Kungiyar Tarayyar Turai, Kwararru a harkar tsaro na kasashe 10 na Sahel da Sahara na duba rawar da fararen hula za su iya takawa a yaki da ta'addanci baya ga matakan soja da ake dauka don tinkarar matsalar.
Ana ci gaba da shirya tarukan mahawara da zummar samo hanyoyin kawo karshen ta'addanci da masu garkuwa da mutane da satar dabbobi a Jamhuriyar Nijar musamman mazauna kan iyakar Katsina, Zamfara da Sokoto da ke Najeriya.
Gwamnatin Nijar ta nemi taimakon jami'an 'yan sanda da sojoji da suka yi ritaya, da su dawo aiki don taimaka mata dakile 'yan ta'adda da suka hana zaman lafiya a kasar.
Matasa 400 da suka fito daga kasashen Afirka ta Yamma takwas, sun gudanar da wani taro a birnin Agadez na Jamhuriyar Nijar domin tattaunawa da nemo mafita kan matsalolin da ke addabarsu.