A cikin shirin za a ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta ce ta bar wa Allah zabi, bayan kotun sauraren korafe-korafen zabe ta yi watsi da bukatar 'yan adawa na yada shari'ar kalubalantar zaben Bola Tinubu kai tsaye ta kafafen yada labarai. Shugaban gidauniyar nan ta Mo Ibrahim ya bukaci kasashen duniya su kawo wa kasar Sudan dauki.