1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Shirin bikin Salla Karama

Salissou Boukari LMJ
May 19, 2020

Yayin da kwanaki kalilan ne suka rage a yi shagulgulan bikin Karamar Salla, biyo bayan gabatowar karshen azumin watan Ramadana, masu sayar da kaji da zabi da ake amfani da su wajen tuwon salla sun ce sun shirya tsaf.

https://p.dw.com/p/3cSs1
Südafrika Hühnerhaltung
Masu sana'ar sayar da kaji da zabi da shirin Karamar Salla a NijarHoto: Getty Images/AFP/R. Jantilal

Duk da cewa wasu mutanen na sayen kaji da zabin ne a jajibirin sallar, wasu na saye ne tun da sauran kwanaki domin su samesu da sauki, sannan su samu kiwata su na kafin yankasu domin yin tuwon salla. Tuni dai masu wannan sana'a suka bazama cikin kauyuka, inda ya zuwa yanzu suka samar da kaji da zabi masu tarin yawa. A baya dai maimakon sayen kaji, wasu na sayen shanu manya-manya su yanka sai su rarraba, wato abin da ake kira watanda. A ganinsu ta haka ne za su iya samun isheshen nama da zai wadaci iyalinsu a lokacin sallar.

A Village Artizanal da ke unguwar Wadata a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, akasari duk shekara suna sayen shanu ne su yanka, amma a bana lamarin ya yi kamari domin matsalar koma bayan tattalin arziki da suka fuskanta. A ranar Asabar ko Lahadi mai zuwa ne dai ake sa ran za ayi shagulgulan Karamar Sallar, inda  tun da sanyin safiya makwabta da sauran dangi da abokan arziki ke yi wa junansu barka da salla, tere da neman gafarar juna kafin zuwa hawan Idi. Sai dai kafin wannan lokaci idanuwa a yanzu sun karkata wajen samun kayayyakin masarafufi da ke kara tashin gauron zabi.