1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 20 da fara shari'ar Musulunci a Najeriya

October 25, 2019

Ranar 27 ga wannan watan na Oktoba ake cika shekaru 20 cif da fara aiki da shari'ar Musulunci a arewacin Najeriya sakamakon kaddamar da shari'ar da gwamnatin jihar Zamfara ta yi a shekarar 1999.

https://p.dw.com/p/3Rxqb
Nigeria Einführung der Scharia Nationalmoschee in Abuja
Hoto: DW/K. Gänsler

A ranar Lahadi 27 ga wannan wata na Oktoba ake cika shekaru 20 da wasu jihohin arewacin Najeriya suka fara aiki da shari'ar Musulunci. A lokacin al'umar Musulmi da yawa a kasar sun yi maraba da matakin. Sai dai wadanda ba Musulmi ba, sun ji takaicin hakan a matsayin tauye musu hakkinsu. Shin ko kwalliya ta biya kudin sabulu shekaru 20 bayan kaddamar da shari'ar ta Musulunci a wasu jihohin arewacin Najeriya?

A ranar 27 ga watan Oktoban shekarar 1999 tsohon gwamnan jihar Zamfara Ahmed Sani Yerima ya sanar da cewa jiharsa za ta fara aiki da shari'ar Musulunci. Wasu jihohin arewacin Najeriya guda 11 ciki har da Kano da Kaduna da ke da rinjayen Musulmi, sun bi sahu. Kiristoci sun yi zanga-zangar adawa da matakin kasancewar ba su san abin da zai biyo baya ba. Hakan ya janyo tashe-tashen hankula da salwantar rayukan dubbai jama'a.

Nigeria Einführung der Scharia
Imam Nuruddeen Lemu na cibiyar Da'wah da ke birnin Minna na jihar NejaHoto: DW/K. Gänsler

Imam Nuruddeen Lemu na cibiyar Da'wah da ke birnin Minna na jihar Neja ya ce tun a lokacin ya ga irin fargabar da sanawar gwamnan ta haifar.

"Hakika akwai fargaba dangane da abin da ta kunsa. Shin babakere ne? Ko tauye hakkin Kirista ne? An samu korafe-korafe da dama da yawan kalamai na nuna kyama. A bangaren Musulmin da ke goyon bayan shari'ar kuma ba a yi wani kokari na a zo a gani don kawar da fargabar ba."

Da yawa daga cikin wadanda ba Musulmi ba na kallon shari'ar a matsayin hanyar keta hakkin dan Adam da masta musu lamba su musulunta. Sai dai Musulmin na jaddada cewa ba za a aiwatar da hukunce-hukuncen shari'ar kan wadanda ba Musulmi ba.

Nigeria Einführung der Scharia
Hoto: DW/K. Gänsler

Shari'ar Musulunci na da dadadden tarihi a arewacin Najeriya, domin tun gabanin mulkin mallakar Birtaniya a karni na 19 an yi amfani da shari'ar a daulolin Sakkwato da Borno, inda kuma ta yi tasiri saboda haka aka ga fa'idarta, kuma aka yi ta kira da dawo da tsarin na Shari'a bayan samun 'yancin kan Najeriya a 1960. Amma hakan ba ta samu ba sai a 1999 lokacin da Najeriya ta koma mulkin farar hula bayan shekaru gommai na mulki soji.

Har yanzu ana wa tsarin na Shari'a a Najeriya kallon wani na siyasa, da 'yan siyasar arewacin Najeriya ke amfani da ita don samun kuri'un jama'a.

Sai dai ga Halima Jibril shugabar kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya wato FOMWAN tsarin Shari'ar ya wuce wani abu na siyasa.

"Lokacin da aka haramta shan barasa duk mai son sha sai ya je kauye ko wajen gari. Hakan ya faranta wa mata rai, domin mazajensu na zuwa gida da wuri bayan sun tashi aiki. Muna ganinsu muna yin abubuwa tare, mun kuma ji dadin haka."

Sai dai shekaru 20 bayan kaddamar da tsarin Shari'ar sauye-sauyen da aka gani a bangaren tsaro da ilimi da samar da ababan more rayuwa kadan ne. Hasali ma damuwar jama'a a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna ita ce garkuwa da mutane a yanzu, kamar yadda Atta Barkindo shugaban cibiyar samar da fahimtar juna tsakanin addinai ta Kukah da ke birnin Abuja ya nunar.

Nigeria Einführung der Scharia Atta Barkindo
Atta Barkindo shugaban cibiyar samar da fahimtar juna tsakanin addinaiHoto: DW/K. Gänsler

"Hakika shekaru 20 bayan fara aiwatar da Shari'a al'amura a arewacin kasar sun kara tabarbarewa. Saboda haka ya kamata a yi mahawara kan batun addini a wannan kasa. Yaya Najeriya a matsayin kasar da babu ruwanta da addini za ta kasance? Yaya Najeriya take a matsayin kasa? Duk wadannan batutuwa ne da ya kamata a yi mahawar kansu."

Akwai bukatar sake yin nazari kan abubuwan da aka alkawarta ganin ingantuwarsu bayan bullo da Shari'a wato kamar ilimi da samar da aikin yi da kuma yaki da cin hanci da rashawa.