1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Dandalin sada zumunta da shawarwari ga mata

Nasir Salisu Zango MNA
June 8, 2021

Mata da dama na neman shawarwari ta dandalin sada zumunta dabam-dabam domin samun saukin rayuwarsu ta aure da sauran zamantakewar rayuwa.

https://p.dw.com/p/3ub13
Symbolbild I BigTech I Social Media
Hoto: Mana Vatsyayana/AFP/Getty Images

Ire-iren matan da ke neman shawarwari ta dandalin sada zumunta ko soshiyal mediya, kance suna samun waraka idan suka aika matsalolinsu a shafukan sada zumunta, 'yan a ji suka tattauna a kai. Sai dai kuma masana na cewar irin wadannan shawarwari na soshiyal mediya ba kasafai ake samun nagari ba domin a kan iya samun gurguwar shawara.

Zuwan shafukan na sada zumunta dabam-dabam ya kawo sauye-sauye a rayuwar al'umma, ta hanyoyi da dama. 'Yan soshiyal mediya da dama sun bude shafuka, inda ake haduwa ana tattauna wasu matsaloli na rayuwa, daga bisani irin wadannan shafukan sun burunkasa sun zama aji, inda ke zama wata mahada da ake kawo matsaloli a tattauna su.

Da yawa na mata sun fi shiga irin wadannan azuzuwa, inda suke kawo matsalolinsu na zamantakewa ana ba su shawarwarin warware su.

Sumayya Sarina ma'abociyar amfani da shafukan sada zumunta ce, ta bayyana cewar a wasu lokutan a kan sami shawara ta gari, amma fa sau da dama a kan saba lamba garin neman gira a rasa idanu.

Ita ma Malama Hadiza Almar'atissalaha a ra'ayin ta cewa ta yi babu fa'idar da za a samu a cikin ajin shafukan sada zumunta don haka a koma asali kawai a huta.

Mata da dama ne dai ke rungumar shafukan sada zumunta tare da neman fatawa ko shawara ga 'yan aji, lamarin da wasu ke cewar ba giringirin ba amma ta yi mai wai kura ta tsinci garaya, wasu kuwa na cewar, su kam sun ga wuri najin dadi shi ne gari ba nasaba ba.