1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharuɗan Ƙungiyar Tarayyar Turai(EU ) na karɓar Turkiya

November 10, 2010

Turkiya ta soki EU bisa sharuɗan da ta gindaya wajen karɓarta a matsayin mamba.

https://p.dw.com/p/Q5Ay
Haɗaɗɗiyar tutar EU da TurkiyaHoto: DW

Ƙasar Turkiya ta yi suka ga Ƙungiyar Tarayyar Turai(EU) game da take-taken da take nunawa a tattaunawar da ake yi game da buƙatarta ta zama mamba ta wannan ƙungiya. Framinstan Turkiya, Recep Tayyip Erdogan ya ce shekaru 50 kenan da ƙungiyar ta bar ƙasarsa tana zaman jira. Ya yi suka ga ƙungiyar bisa sauya sharuɗan karɓar sabuwar mamba. A cikin rahotonta na shekara shekara game da ci-gaban da take samu, hukumar zartarwar Ƙungiyar Tarayyar Turai ta nemi Turkiya da ta ƙara kare haƙƙin mata da tsirarun ƙabilu na wannan ƙasa. Ƙungiyar ta ƙara da cewa babu wani ci-gaba na azo a gani da Turkiya ta samu wajen warware rikicin da ke tsakaninta da ƙasar Cyprus, wanda shi ne ke karan tsaye ga yunƙurin Turkiya na haɗewa da Ƙungiyar Tarayyar Turai.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu