Shari′ar mayakan Boko Haram a Najeriya | Siyasa | DW | 09.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shari'ar mayakan Boko Haram a Najeriya

A ranar Litinin ne gwamnatin Najeriya ke fara shari’ar 'ya'yan kungiyar Boko Haram fiye da 1,600 da ake zargi da laifuffuka daban-daban na ta’adanci.

Wannan shari'a da aka dade ana jiran lokacin da za'a farata, mahukuntan Najeriyar sun bayyana cewa za'a yita ne a kebabbun wuraren da ake tsare mutanen da ake zargi farawa da na garin Kainji da ke jihar Niger da kuma Maiduguri a jihar Borno a asirce, inda tuni gwamnatin ta samar da alakali hudu da za su jagoranci tuhumar da take yiwa 'ya'yan kungiyar ta Jama'atu Ahlu Sunnah li Da'awati Waljihad. A baya gwamnati ta yi koken fuskantar kalubale da suka hada da rashin kyakyawan tsaro da rashin cikakken bincike a kan wadanda ake zargi saboda yakin da ake yi da dai sauransu. Ko a yanzu ta shirya sosai  da ma shawo kan matsalolin? Malam Abubakar Malami shi ne ministan shari'a kuma antoni janar na Najeriyar ya ce ma'aikatar shari'ar kasar ta yi tanadi sosai kan wannan shari'a.

Duk da cewa za'a dogara ne a kan dokar yaki da ayyukan ta'adanci ta Najeriyar da aka yiwa gyaran fuska da ma sauran dokokin kasa. Shin a bisa tanade-tanade za'a samun nasarar tuhumar masu laifin bisa gaskiya da kamanta adalci? Barrsiter Mohammed Shuaibu lauya ne mai zaman kansa da ke Abuja ya ce shedu da hukumomi za su gabatar shi ne nasarar shari'ar ko akasin haka.

Kungiyoyin kasa da kasa na sa ido a kan yadda za'a gudanar da wannan shari'a da za'a yi ta a asirce ba tare da barin ‘yan jaridu ba. Abin jira a ganin shi ne yadda gwamnatin Najeriya za ta aiwatar da wannan shari'a da ke daukan hankali sosai musamman kokari na kamanta adalci sanin cewa gwamnati ta ce tuni an wanke mutane 220 saboda rashin cikakkiyar shaidar suna da wani laifi. Ayyukan ta'adanci dai na zama sabon lamari a Najeriya da kasashen Afirka ta Yamma da dama.

 

Sauti da bidiyo akan labarin