1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Zabe da ya sauya siyasar Jamus

October 15, 2018

Jami'yyar CSU ta ga mummunan koma baya a zaben jihar Bavaria na ranar Lahadi. Wannan sakamako zai yi matukar tasiri ba ma a Bavaria kadai ba, har ma da tarayya baki daya kamar yadda Rosalia Romaniec ta DW ta nunar.

https://p.dw.com/p/36Zgt
Landtagswahl Bayern - ZDF-Runde
Hoto: picture-alliance/dpa/L. Barth-Tuttas

Wannan zabe a cewar Rosalia Romaniec cikin sharhin da ta rubuta ya sauya fasalin al'amura kwarai ba kawai a jihar Bavaria kadai ba. Tsawon shekaru da jam'iyyar Christian Social Union CSU ta kwashe tana mulki tare da samun karbuwa a matsayin jam'iyyar 'yan mazan jiya. Jam'iyyar ta fado daga matsayin kusan kashi 48 cikin dari da ta ke kai ada zuwa kashi 37.2 cikin dari, matakin da ba zai yiwu ka iya kau da kai akansa ba.  Kaye ne mummuna kuma mai ciwo. Rosalia ta ce wannan shan kaye na CSU ba wai nasarar sauran jam'iyyu ne ta kawo haka ba, a'a illa shugabancin jam'iyyar da ya kamata ya zargi kansa da kansa da wannan koma baya.

Babban abin mamaki da wannan sakon zaben shi ne nasarar da jam'iyyar masu rajin kare muhalli the Greens suka samu da kashi 17.5 cikin dari sun rubanya matsayin da suke kai a Bavaria kuma sun kama hanyar zama babbar jam'iyya ta biyu hatta a matakin tarayya.

A jihar ta Bavaria dai magoya bayan CSU sun yi sauyin sheka zuwa the Greens watakila saboda sun dauki akidar koyarwar addini da CSU din ta dogara akansa na "so dan uwanka kamar son kanka" kan batun da ya shafi 'yan gudun hijira. Sun dauki wannan tafarkin fiye da 'yan mazan jiyan. Musamman shugaban jam'iyyar ta CSU Horst Seehofer wanda shi ne ministan cikin gidan Jamus, ga alama ya manta amma masu kada kuri'a da dama sun ki yarda kokarin jan ra'ayinsu na sanya musu tsoro a zukata kan yaduwar Musulmi inda suke cewa nuna tausayi da yakana ga dan uwanka ya fi gaban komai.

Deutschland Reaktionen auf Bayern Wahl Söder und Seehofer in München
Söder da Seehofer jiga-jigai a jam'iyyar CSUHoto: Getty Images/AFP/O. Andersen

Wata jam'iyyar da ta yi galaba a zaben ita ce jam'iyyar AfD mai akidar kyamar baki. wannan bai ba da mamaki ba ko kadan. A yanzu jiha ta 15 kenan da ta sami shiga majalisar dokoki daga cikin jihohi 16 na tarayyar Jamus. Wannan kuwa ya faru ne saboda manufar da ake ciki a halin yanzu kan 'yan gudun hijra. Abin takaici ne yadda suka sami kashi 10 cikin dari na kuri'u ko da yake ma an yi fargabar cewa suna iya samun kashi 20 cikin dari. Sakamakon ba wai ya nuna jama'a sun karkata ba ga tsatstsauran ra'ayin rikau sun dai nuna bujirewa ne don bacin rai ga kuskuren da CSU ta tafka.

Shekaru da dama Jihar Bavaria tana bin tafarkin jagoranta Franz-Joseph Strauss wanda ya taba cewa wajibi ne a wanzar da halastacciyar jam'iyya ta dimukuradiyya a siyasar Jamus bisa akidar 'yan mazan jiya ta CSU tare da abokiyar kawancenta CDU. Wannan ya yi tasiri tsawon shekaru kafin a baya bayan nan da shugabaninta suka firgita suka shiga kwaikwayon manufofin jam'iyyar AfD mai kyamar baki a bana. Kafin su farga da wannan kuskuren tuni masu adawa da Shugabar gwamnati Angela Merkel suka yi musu illa. Seehofer ya yi kasada amma kuma wannan shi ne sakamakon da ya girba.