Sharhi: Wa zai yarda da Najeriya? | Siyasa | DW | 08.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sharhi: Wa zai yarda da Najeriya?

Mako guda kafin a gudanar da babban zaben Najeriya, hukumar INEC ta dage zaben, da tsawon makonni shida. Sai dai dalilan da ta bayar ba masu gamsarwa ne sosai ba, inji Thomas Mösch a cikin wannan sharhi.

Matakin dage zaben ya bar baya da kura. Ko da yake a kwanakin nan ya fito fili cewa hukumar zaben mai zaman kanta ta INEC ba ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaben ba, amma shugabanta Farfesa Attahiru Jega bai yi nuni da wadannan matsalolin a matsayin dalilin dage zaben ba. Maimakon haka ya dage cewa hukumar ka iya gudanar zaben kamar yadda aka shirya tun farko wato 14 ga watannan na Fabrairu.

Rashin tsaro ne dalilin daukar wannan mataki

Yanzu an dauki matakin dage zaben saboda dalilai na rashin tabbatar da tsaron lafiyar jami'an zabe da masu kada kuri'a, wanda ya ce dakarun tsaron kasar ne suka yi masa bayani. Domin suna son su kaddamar da wani gagarumin farmaki a kan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya, kuma bisa wannan dalili ba za su iya tabbatar da tsaro a fadin kasar lokacin zaben ba. Sai dai dalilan nan da ya bayar sun saka ayar tambayoyi da yawa.

Matakin na INEC ya bar baya da kura inji Thomas Mösch shugaban sashen Hausa na DW

Matakin na INEC ya bar baya da kura inji Thomas Mösch shugaban sashen Hausa na DW

Da farko dai shi wane abu ne sabo cikin maganar cewa ba za a iya tabbatar da tsaron lafiyar masu kada kuri'a ba? Tun watanni da yawa da suka wuce wasu yankunan arewa maso gabashin Najeriya ke karkashin ikon Boko Haram, wadanda kuma ke ci gaba da kai hare-hare a wasu wurare na kasar. Amma duk da haka masu ruwa da tsaki sun yi ta nanata cewa za su iya gudanar da zaben.

Na biyu shi ne shin mai yasa sai yanzu dakarun tsaron suka samu basirar kai babban farmaki a kan Boko Haram da zai hannasu tabbatar da tsaro a sauran yankunan kasar? Wai shin wane tabbaci suke da shi cewa za su iya magance ayyukan tarzoman cikin makonni shida, bayan sun kwashe shekaru biyar ba su kai gaci ba?

Dalilan sun yi rauni

Daukacin 'yan Najeriya dai ba su gamsu da hujjojin da Jegan ya bayar yanzu ba. Kasancewa ma an yi ta samun sabanin tsakanin gwamnati da 'yan adawa game da ranakun shirya zabubbukan. Yayin da da yawa daga cikin kananan jam'iyyu da kuma jam'iyyar PDP ta shugaban kasa Goodluck Jonathan suka goyi bayan bukatar dage zaben, ita kuwa babbar jam'iyyar adawa ta APC karkashin dan takararta Muhammad Buhari, ta ki. Kwanaki masu zuwa za su nuna ko kasar za ta jure wa wannan rarrabuwar kawuna.

INEC ta dogara ga bayanan dakarun tsaro, to amma mai zai faru idan a cikin makonni shida rundunar ta sake ba da shawara a dage zaben? Gudanar da zaben a cikin watannin Maris da Afrilu bai saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya ba, wanda ya tanadi rantsar da shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu. Amma idan sojoji da 'yan sanda da kuma hukumomin tsaro suka ci gaba da dakatar da zaben, to hakan na barazanar ta da wani wani rikici game da kundin tsarin mulkin kasar. Kasancewa farin jinin shugaba Jonathan na raguwa idan aka kwatanta da shekaru hudu baya, masu sukar lamiri na fargabar cewa yana da niyar amfani da dalilan rashin tsaron don kar a gudanar da zaben.

Shin yanzu za a matsa kaimi a yaki da Boko Haram?

Duk da haka dai akwai wasu bayanai masu gamsarwa. Shekaru hudu da suka gabata Farfesa Attahiru Jega ya nuna cewa shi mutum ne da ke iya daukar kyakkyawan mataki idan shi ne mafi a'ala ga samun zabe mai inganci. A ranar farko ta zaben 2011 ya dakatar da zaben saboda wani rudani da aka samu. A karshe an samu nasarar ci gaba da zaben ba da matsala ba.

A bangaren sojin ma an samu ci gaba a farkon wannan wata bayan da kasashe makwabtan Najeriya musamman Chadi suka fara kai farmaki kan Boko Haram a kan iyaka da Najeriya. Watakila rundunar Najeriya ta ga yanzu tana da wata damar samun nasara cikin kankanen lokaci. Fata dai shi ne komai yayi kyau kamar shekaru hudu da suka wuce.

Sauti da bidiyo akan labarin