Scotland za ta koma cikin kungiyar EU | Labarai | DW | 01.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Scotland za ta koma cikin kungiyar EU

Bayan da Birtaniya ta kammala ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai EU, al'ummar yankin Scotland na Birtaniyan na karfafa fatan sake koma wa cikin kungiyar ta EU.

Schottland Ministerin Nicola Sturgeon

Nicola Sturgeon Firaminstar yankin Scotlan na Birtaniya

Firaminstar yankin Nicola Sturgeon ta rubuta a shafinta na Twitter cewa: "Ba da jimawa ba Sotland za ta koma cikin EU, ku rubuta ku ajiye." Masu fafutuka na yin zanga-zanga cikin dare a Edinburgh da nufin neman ficewar yankin na Scotland daga Birtaniya domin samun 'yancin cin gashin kai. Yayin kada kuri'ar raba gardama dangane da ficewar Birtaniyan daga EU a 2016, da dama daga al'ummar yankin na Scotland sun zabi ci gaba da zama a EU din.