1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Scholz: Putin ya rage barazanar amfani da makaman nukiliya

December 8, 2022

Scholz ya ce matsin lamba ce ta sanyaya wa shugaban Rasha gwiwa wajen barazanar amfani da makamai masu guba. Sai dai duk da haka, Scholz ya ce akwai bukatar Turai da Rasha su ci gaba da tattaunawa kan Ukraine.

https://p.dw.com/p/4KdiC
Hoto: Markus Schreiber/AP/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce shugaban Rasha Vladimir Putin ya rage barazanar amfani da makamin nukiliya a yakin da Rasha ke yi da Ukraine. Shugaban na Jamus ya fadi haka ne a yayin wata tattaunawa da aka yi da shi albarkacin cikarsa shekara guda a kan karagar mulki.

A ranar Laraba ce dai Shugaba Putin ya ce fargabar amfani da makamin nukiliya a rikicin Ukraine na kara karuwa amma ya jadadda cewa Rasha na cikin hayyacinta, a saboda haka ba za ta fara amfani da shi ba har sai idan bukatar hakan ta taso wajen kare kanta.