Sauyi a kafafen yada labarai na Najeriya | Labarai | DW | 15.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sauyi a kafafen yada labarai na Najeriya

Gwamanatin Najeriya ta sanar da sauke shugabanin hukumomin yada labaru na kasar daga aikinsu a mataki na gudanar da sauye-sauyen da aka dade ana jiran faruwarsu.

Sanarwar da ministan yada labaru na tarayyar Najeriya Lai Muhammad ya fitar, ta bayyana cewa shugabanin da abin ya shafa sun hada da Darakta Janar na gidajen rediyon Muryar Najeriya da na Radio Najeriya da kuma na gidan Telbijin na kasa NTA. Sai shugaban kamfanin dillancin labaru na Najeriyar NAN da kuma Hukumar Wayar da kan Jama’a .

Jinkirin gudanar da sauye-sauyen tun hawan gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ya sanya fuskantar matsin lamba. Sai dai masu sharhi kan harkokin yau da kunlun a Najeriya sun ce wannan canji ya yi daidai ganin yadda kafofin yada labarai suka kasance wata hanya ta kusa da al'ummar kasa.