1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauya kwamandan yakar Boko Haram a Najeriya

Yusuf Bala Nayaya
November 12, 2018

Rundinar sojan Najeriya ta nada sabon kwamanda da zai jagoranci yaki da Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, yankin da hare-hare kan jami'an tsaro ke kara ta'azzara a watannin baya-bayan nan.

https://p.dw.com/p/3875m
Nigeria Militär Tukur Yusuf Buratai
Hoto: NPR

Manjo Janar Benson Akinroluyo zai maye gurbin Manjo Abba Dikko domin jagorantar rundinar sojojin nan ta Operation Lafiya Dole, da ke fafutikar samar da zaman lafiya kamar yadda sojojin suka sanar a karshen mako. Akinroluyo ya kasance kwamanda na biyar kenan cikin shekaru biyu da aka sake cikin jagororin yaki da Boko Haram wadanda ke kai hare-hare sansanoni na sojoji da ma yin nasara ta halaka wasu sojojin.

Dikko dai da aka maye gurbinsa ya fara aikin jagorantar rundinar ta Lafiya Dole ne a watan Yuli, tun kuma lokacin da ya hau karagar jagorancin an kai hare-hare kan sansanonin soja sau tara mafi akasari a arewacin jihar ta Borno kusa da Tafkin Chadi.