1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dabarun yakar 'yan ta'adda a Nijar

Salissou Boukari YB
May 22, 2019

Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar ya yi wani zama da manyan jami'an tsaro na Nijar da jakadun kasashen Amirka da Faransa don duba hanyoyi na tunkarar kalubalen tsaro da ya addabi kasar.

https://p.dw.com/p/3IuYF
Soldaten im Niger
Hoto: Desmazes/AFP/Getty Images

A ranar Laraba ce majalisar tsaro ta kasa a Jamhuriyar Nijar ta yi wani zama na musamman a karkashin jagorancin Shugaba Mahamadou Issoufou, tare kuma da halartar jakadun kasashen Amirka da Faransa da ma manyan sojoji na wadannan kasashe, gami da na Nijar. Wannan zama dai an yi shi ne da zummar sake dubaru da karfafa hadin gwiwa domin yakar ‘yan ta’adda da ke neman mayar da kasar ta Nijar wani filin daga.

Har ila yau zaman na zuwa a daidai wannan lokaci da al’ummar Nijar ke cikin juyayin rashin da aka yi na sojoji kimanin 28 da ‘yan ta’adda suka hallaka a yankin iyaka da kasar Mali.

Tun dai da jimawa ne daga cikin ‘yan kasar ta Nijar ke zargin kasashen ketare musamman ma na Faransa da Amirka da yin babakere a kasar ta Nijar amma kuma bai hana ana kai hari ga kasar ta Nijar har ma da kashe mata sojoji ba. Sai dai wannan zama an yi shi ne domin kawo gyara a fannin hulda ta tsaro da siyasa tsakanin kasashen na Faransa da Amirka wanda duk da cewa suna nan cikin kasar ta Nijar amma kuma suna yaki ne a wata kasa kamar Mali. Kalla Moutari Shi ne ministan tsaron kasa na Jamhuriyar Nijar ya ce sun kira dakarun na kasashen waje don idan suna bukatar taimako su kawo masu dauki.

Mali Straße zur Grenze des Niger
Nijar dai na tsaurara matakai na tsaro a iyakartaHoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

Da yake magana a lokacin wannan taro, jakadan Amirka a kasar ta Nijar Eric Whitaker ya jaddada aniyar Amirka ta aiki hannu da hannu da kasar Nijar domin yakar ta’addanci da duk wani abun da ke haddasa ta’addancin.

Shi kuma daga na shi bangare Mista Alexandre Garcia, jakadan kasar Faransa a Nijar bayan ya jaddada aniya kasar Faransa ta kawo tallafi ga sojojin na Nijar, ya kuma yaba kwazon da sojojin na Nijar suke da shi a faren daga.

Ana sa ran dai wannan zaman taro na majalisar tsaron kasar ta Nijar da aka yi shi tare sojojin kasashen na Amirka da Faransa gamai da jakadun wadannan kasashe, zai sa a gani a kasa a nan gaba a yakin da ake yi da ‘yan ta’adda masu tayar da zaune tsaye a Nijar.