Mayakan kawance da saudiyya ke jagoranta a kasar Yemen sun sanar da kai wani farmaki a sansanin mayakan Huthi da ke Sana'a babban birnin kasar a wannan Lahadi, inda suka kashe mutane uku.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Saudiyya SPA, a wannan harin an yi nasarar lalata makamai da dama da ma mabuyar mayakan na Huthi. Wannan na zuwa ne bayan da a ranar Asabar, hukumomi a Saudiyya suka sanar da wasu harin rokoki da ake zargin mayakan Huthi da harbawa a masarautar Saudiyya wanda ya yi sanadin rayukar mutane uku da kuma jikkata wasu da dama. Harin da ke zama irinsa na farko ga masarautar a sama da shekarun uku.
Saudiyya dai ta jima tana zargin kasar Iran da daukar nauyin ayyukan mayakan na Huthi da ma samar musu da manyan makamai. Tun a shekarar 2014 ne Yemen ta fada cikin yaki tsakanin gwamnati da mayakan na Huthi da ke rike da ikon yankunan arewacin kasar.