Saudiyya ta son tsagaita wuta a Yemen | Labarai | DW | 22.03.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saudiyya ta son tsagaita wuta a Yemen

Kasar Saudiyya ta sanar da shirinta na yi wa 'yan tawayen Huthi da ke Yemen tayin tsagaita wuta a kasar da ta shafe shekaru tana gwabza yaki tare da bude filin jiragen sama na babban birnin kasar Sanaa.

Bayan da Saudiyya ta sanar da shirin yi wa 'yan tawayen Huthi da ke Yemen tayin tsagaita wuta ta shigar da abinci da man fetur ta tashar jirgin ruwan Hodeida. Wannan babban mataki ne da masarautar Saudiyya ta dauka da zai kawo karshen yakin da ya daidaita kasar Yemen, kasa mafi talauci a daular Larabawa.

Saudiyyar ta dau wannan matakin ne bayan da 'yan tawayen Huthi suka kara matsa kaimi kan kaddamar da harin makami mai linzami kan yankin da ke da arzikin mai na masarautar tare da kokarin dawo da martabarta a idon Amirka karkashin shugabancin Joe Biden. Sai dai a cewar ministan harkokin wajen masarautar Faisal bin Farhan zabi ya rage wa 'yan tawayen na kare matarbarta ko kuma ta Iran.