Saudiyya ta jagoranci tura dakaru Yemen | Siyasa | DW | 26.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Saudiyya ta jagoranci tura dakaru Yemen

Tuni dakarun suka fara kai hare-hare ta sama, abin da ke sanya fargaba a zukatan 'yan yankin da dama wadanda suke gani matakin zai fadada rikicin.

Hadin gwiwar kasahen larabawa a karkashin jagorancin kasar Saudiyya sun yanke shawarar fara aikawa da dakarun su kasar Yemen bisa bukatar shugaba Abdu Rabo Hadi Mansur domin fatattakar masu jihadi wadanda ake yi wa kallon yan ta'adda, a yayin da a waje guda kuma barin wutar da ake yi a birnin Sanaa ya tilastawa dubban mutane ficewa daga birnin.

Jemen Zerstörung in Sanaa nach dem Luftangriff

Da yawa sun fara tserewa sakamkon hare-haren ta sama

Wannan batun shi ne dai zai kasance muhimman batun da taron kasahen Larabawa zai duba a ranar Asabar mai zuwa, kuma Kungiyar Kasahen Larabawa ita ce ta gabatar da wannan kudiri a yunkurin da take yi na yaki da taddanci.

Sai dai kawo yanzu dakarun kasar Saudiyya sun soma barin wuta a kokarinsu na sake karbe madafun iko daga hannu yan tawayen Houthi.

Majiyoyin tsaro, da kuma shaidu sun ce wurare da dama wadanda ke cikin hannun dakaru na birnin Sanaa, a ciki har da wani sansanin mayaka, a fadar shugaban kasar sun fuskanci luguden wuta na hare-haren Saudiyar da kawyenta abin da ya sa a yau kwana daya bayan harin dubban jama ke ta tserewa daga birnin.

'Yan tawaye sun ce ba za su ja da baya ba.

A halin da ake ciki dai an rufe makarantu wadanda kawo yanzu ba a bayyana ranakun da za a bude su ba. A gumurzun da aka sha a jiya a kudancin na Yemen tsakanin magoya bayan Mansour Hadi da 'yan tawayen yan Shia na Houthis mutane 18 suka mutu a lardin lahje.

Muhammad Al-Buhari daya daga cikin shugabannin 'yan tawayen ya ce ba zasu ja da baya dangane da hare haren na hadin gwiwa da ake kaimusu

"Da karfin ikon Allah za mu murkushe wannan gwamnati ta mulkin danniya sannan ya ce ina yin kira ga jama'a fara rhula da su gane cewar ba da su muke ba kuma muna neman hadin kansu"

Jemen Treffen der Außenminister der Arabischen Liga

Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa na ganawa kann batun

Gwabzawar da aka yi dai ta lardin na Alhouta ta afku ne lokacin da yan tawayen Houthis din suka ci karo da mayan gwamnatin a kusa da wani caji ofis kafin daga, tun da farko sojojin da aka baza a yanki sun arce daga cikin sansanonisu tare da barin makamai da motoci dangane da yadda yan tawayen suka sha karfinsu. Riyad Yassin shi ne ministan harkokin waje na Yemen

"Mun mika bukatarmu ga taron kasahen yankin Larabawa wadanda zasu tattauna ranar Asabar domin mu samu dauki a kan wannan tashin hankali"

Shugaba Barack Obama dai na Amirka ya goyi bayan hare-haren na Saudiyyya a Yemen da nufin sake kwace mulki sannan sakataran harkokin wajen Amirka John Kerry a hirasa ta wayar tarho da takwaransa na yankin Gulf ya ce Amirka za ta taimaka ta hanyar samar da bayanan siri ga sojojin kawancen.

Sauti da bidiyo akan labarin