1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Yadda annobar Coronavirus ta rage yawan mahajjata

Ramatu Garba Baba
July 27, 2020

Musulmi kimanin dubu goma da suka kasance ko 'yan asalin kasar ko kuma baki da ke zaune a cikin kasar ne, za su samu damar gudanar da aikin hajjin bisa wasu tsauraran ka'idoji da aka gindaya a yayin gudanar da ibadar. 

https://p.dw.com/p/3fyvv
Saudi-Arabien einsame Pilger in Mekka an der Kaaba
Hoto: AFP

A Saudiyya, maniyyata sun shirya soma gudanar da aikin hajjin bana da annobar Coronavirus ta janyo takaita yawan al'ummar musulmin da ke da niyyar zuwa. Mutum dubu goma kacal da suka kasance ko 'yan asalin kasar ko kuma baki da ke zaune a cikin kasar ne, za su samu damar gudanar da aikin hajjin bisa wasu tsauraran ka'idoji da aka gindaya a yayin gudanar da ibadar. 

Saudiyya ta kasance daya daga cikin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da ake da yawan alkaluman masu cutar ta Covid-19, inda tuni cutar ta kashe mutum dubu biyu da dari bakwai da talatin da uku daga cikin sama da dubu dari biyu da sittin da ta kama.


Wannan shi ne karon farko da ake daukar mataki na hana maniyyata daga sauran kasashen duniya shiga aikin hajjin a tarihi. Ma'aikatar shirya aikin hajjin dai, ta ce ya zama dole a yi hakan, saboda fargabar yada cutar Coronavirus.