1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarki Sanusi ya yi Juma'ar farko a sabon mulki

May 24, 2024

Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II ya tunasar da mabiya addinin Islama bukatar komawa ga Allah tare da yin addu'o'i a lokacin da ya jagoranci sallar Juma'a a gidan gwamnatin Kano.

https://p.dw.com/p/4gGaV
Hoto: Aminu Abubakar/AFP/Getty Images

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya jinjina wa gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf da 'yan majalisar jihar kan mayar da shi karagar mulkinsa da suka yi. Sarki Sanusi ya fadi haka ne a Juma'ar nan jim kadan bayan da ya karbi takardar da ke tabbatar da dawo da shi kujerarsa.

''A cikin sarakunan Kano, an fara irin wannan ne daga kan Bagauda sama da shekaru 1,000 da suka wuce. A cikin wadannan shekaru sau daya ne aka samu wani sarki Muhammadu Koguna wanda aka sauke shi bayan wasu 'yan kwanaki ya dawo kujerarsa. Wannan ya nuna cewa a cikin shekaru 1,000, ba a taba samun irin abin da ya faru da ni ba.'' in ji sabon sarkin na Kano wanda yanzu ake wa lakabi da sarki na 16 bayan da a baya ya zama sarki na 14.

Bayan kammala karbar takardar dawowa gadon sarautar Kano, sarkin ya jagoranci sallar Juma'a a babban masallacin gidan gwamnatin Kano, inda ya yi huduba kamar yadda sauran limaman Juma'a ke yi tare da jagorar salllar. Wannan ita ce kuma Juma'arsa ta farko tun bayan da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana shi a matsayin sarkin kano na 16. Kafin sauke shi daga wannan kujera a shekara ta 2020, Sarki Sanusi, na da irin wannan al'ada ta jagorantar sallar Juma'a a masallacin da ke fadarsa.

A fadar sarkin Kanon, jama'a da dama ne suka halarci babban masallacin kofar gidan sarkin domin yin sallar Juma'a da sarki Muhammadu Sunusi II wanda da farko aka bayar da sanarwar cewa shi ne zai jagoranci sallar amma sai sarkin ya yi sallar a fadar gwamnatin jihar Kano tare da gwamna Abba Kabir Yusuf. Amma duk da haka wakilinmu Abdulrahman Kabir ya ce rashin zuwan sarkin bai hana mutane cika masallacin na Juma'a da ke gidan sarki ba.

Yadda Sarki Sanusi ya dawo kujerarsa

Majalisar dokokin jihar Kano ce ta sake yi wa dokar masarautun jihar gyaran fuska a cikin kasa da kwanaki uku, daga karshe gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yuusf ya sake dawo da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano a ranar Alhamis 23 ga watan Mayu na 2024.

Wannan na zuwa ne bayan dogon lokacin da aka kwashe ana jita-jitar hakan za ta faru. Tuni 'yan majalisa na jam'iyyar adawa ta APC suka yi watsi da sabuwar dokar da suka ce za ta kuntata wa mutanen karkara wadanda tun da farko tsohuwar gwamnatinsu ta ce ta rarraba masarautar domin su.